Yan bindiga dadi sun harbi surukin tsohon shugaba Jonathan a Calabar

0

-Yan bindiga dadi sun harbi surukin tsohon shugaba Jonathan a Calabar

-Yan sanda sun lashi takobin binciko duk wanda suke da hannu a harin

-Wannan dai shine karo na uku da ake kai ma surukin shugaban hari

Yan bindiga dadi sun harbi surukin tsohon shugaban kasaGoodluck Ebele Jonathan, Prince Goodwill Edward a ranar juma’a a garin Calabar na jihar Cross rivers.

A bada rahoton cewa an harbe Edward ne a gidan sa da ke rukunin gidajen calabar municipal axis da ke babban birnin cross river, wato Calabar.

Yan bindiga dadi sun harbi surukin tsohon shugaba Jonathan a Calabar

Yan bindiga dadi sun harbi surukin tsohon shugaba Jonathan a Calabar

Edward shine mai bada shawara na musamman akan harkokin matasa na gwamna ben Ayade.

Rahotani basu bada bayanin irin raunin da yaji ba, sai dai a yanzu yana karban magani a wata boyeyen asibiti a garin na Calabar.

KUMA KU KARANTA: Kun ji yaushe Lionel Messi zai bar kungiyar Barcelona?

Shi dai Edward dan asalin karamar hukumar Abi ne na jihar Cross river, ya auri diyar tsogon shugaba Jonathan a wani gagarimin biki da akayi a shekara ta 2014.

An tutunbi kwamishinan yan sandan jihar, Mr. Hafiz Inuwa akan lamarin, amma yace babu wanda ya kawo musu rahoton faruwan lamarin a rubuce. Amma yace wannan bashi ne lokaci na farko da Edward din ya taba fuskantar irin wannan harin ba.

Inuwa yace, “Sun taba kai masa hari, wannan shine na uku ko hudu da ake kai masa harin, amma abin mamaki shine ba wanda ya taba shigar da kara a offishin yan sanda akan al’amarin. Baza mu jira har sai an shigar da kara ba domin mun san nauyin da ya rataya akan mu a matsayin yan sanda.

Ko da suna da wasu dalilan da yasa basu kawo kara wurin mu, aikin mu ne muyi bincike akan al’amarin kuma da yardan Allah zamu gano wanda suka aikata wannan danyen aikin.

“Yanzu ake bani bayannin cewa wannan shine karo na uku ko hudu da ake kai masa irin wannan harin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Culled from here

Share.

About Author

Comments are closed.